SHEIKH AMINA DAURAWA lectures logo SHEIKH AMINA DAURAWA lectures

SHEIKH AMINA DAURAWA lectures

by AdamsDUT

🗂️ Music & Audio

🆓 free

4.9/5 ( 650+ reviews)
Android application SHEIKH AMINA DAURAWA lectures screenshort

Features SHEIKH AMINA DAURAWA lectures

Wannan application yana dauke da wasu zababun lekcoci daga sheikh aminu ibrahim daurawa ke gabatarwa.shine muka ga ya dace muyi application wanda mutane zasu su saurara a saukake.Allah ya sakawa Sheikh ibrahim aminu daurawa domin yayi kokari wajen yayi kokari wajen yada ilimin Allah da na manzon sa domin karuwar alumar musulmai.
Mukuma Allah ya bamu ikon ji da kuma amfani daga abin da muka saurara.Bayan lectures na Sheikh ibrahim aminu daurawa akwai kudin tarihi kashi na daya da na biyu by Sheikh ibrahim aminu daurawa duk a cikin wannan manhaja idan akayi duba.Akwai karatun malam Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 akan illar harshe,matsalolin aure by Sheikh ibrahim aminu daurawa mp3 dai sauransu.za kuma a iya samun wasu karatuttukan na wasu malam irin su sheikh jafar mahmud adam, sheikh albani zariya,sheikh ali isah fantami, shiekh kabir gombe.Wasu daga cikin karatuttukan sheikh jafar da za a samu idan akayi searching Adamsdut a play store.Siffatus salatin nabiyyi sheikh jafar Arbauna Hadith sheikh jafar mp3 Bulugul maram sheikh jafar mp3 Kitab Tauhid sheikh jafar mp3 Umdatul ahkamKitab at tauhid HausaAkwai karatun alqurani na wasu manyan makaranta kamarcomplete quran offline by sheikh abdulrahman al-sudaisbeautiful quran recitation by sheikh maher almuquiycomplete quran offline by shiekh abdolbasitquran recitation by mishary alfasy mp3 offline and so on.Don allah idan har kaji dadin wannan kundin tarihi by Sheikh ibrahim aminu daurawa to kayi sharing din sa ga sauran yan uwa musulmai domin suma su samu su amfana.kuma kada a manta a yi rating kudin tarihi by Sheikh ibrahim aminu daurawa.kadan daga cikin tarihin Sheikh ibrahim aminu daurawa,TARIHIN SHEIK AMINU DAURAWA KANO :-Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal.
Mahaifinashahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Fagge.
Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa datsohuwar tashar kuka.
Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai.
Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala.
Na fara karatun Alqur’ani mai girma tun ina dankarami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15.
Bayan firamare da sakandare, dana yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyanmashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimida fannoninsa daban-daban.
Wadannan manyan malamai su ne:1.
Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.2.
Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.3.
Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.4.
Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.5.
Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.6.
Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.7.
Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir awajensa.8.
Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.9.
Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.10.
Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.11.
Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh awajensa.
Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa.
Allah ya jiqansa da rahama!12.
Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa.
Wannan malami, awajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya.
Malami ne maihaquri da juriyar karantarwa.da dai sauran malamai daban daban a duniya.

Secure & Private

Your data is protected with industry-leading security protocols.

24/7 Support

Our dedicated support team is always ready to help you.

Personalization

Customize the app to match your preferences and workflow.

Screenshots

See the SHEIKH AMINA DAURAWA lectures in Action

SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Screen 1
SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Screen 2
SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Screen 3
SHEIKH AMINA DAURAWA lectures Screen 4

Get the App Today

Download on Google Play

Available for Android 8.0 and above